
Tauraruwar fina-finan Hausa, Rashida Mai Sa’a ta bayyana cewa tunda ake a Kannywood, ba’a taba yin Mawakin da ya kai Rarara ba.
Ta bayyana hakane a matsayin martani ga Naziru Sarkin Waka a yayin da yace motarsa tafi ta Rarara kudi nunki 3.
Rashida tace wannan motar da Naziru ke gasa da ita daya ce daga cikin motocin Rarara masu tsada.
Ta bayyana cewa, Rarara ya taimaki jama’a da yawa amma tana son Naziru ya fito ya fadi mutum daya daya taimakawa, tace duk yaran dake kasanshi sun tsere.