
Farfesa Jerry Gana ya bayyana cewa idan Peter Obi ya koma PDP ya tsaya takarar shugaban kasa, babu dan takarar shugaban kasa daga Arewa da zai iya kayar dashi.
Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi.
Yace suna kan kokarin ganin sun jawo hankalin Peter Obi ya klma jam’iyyar su ta PDP.
Yace kuma bayan Peter Obi din, akwai wani ma wanda yafi Peter Obi nagarta da karbuwa da suke kokarin kawowa PDP ya musu takara.