
Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu yayi martani kan rahotannin dake cewa ya gina gidansa ne a shekaru biyu bayan da ya zama Minista.
Da yake magana ta bakin me magana da yawunsa, Mr. Femi Awogboro, Ministan yace maganar gaskiya ya kammala ginin gidanne a shekarar 2023, wata daya kamin a nadashi minista.
Ministan ya kuma nuna hotuna a matsayin shaidar ikirarinsa inda yayi kiran cewa, tun kamin ya hau mukamin Minista ya gina gidan.
An dai rika tambayar ina ya samu kudin gina katafaren gida haka shekaru 2 kacal da zamansa minista?