Kankana na da matukar amfani sosai a jikin dan Adam musamman mata. A wannan rubutu, zamu bayyana amfanin Kankana a jikin mata.
Da farko dai kankana na da Sinadaran Vitamins A, B6, da C wanda suke karawa fata sheki, da lafiya.
Hakanan tana maganin bushewar fata, da maganin ciwon daji watau Cancer.
Ga mata masu ciki, Kankana na taimakawa sosai wajan nakuda da hana bari da haihuwar bakwaini.
Kankana na daya daga cikin kayan itatuwan da masana ilimin kimiyyar lafiya ke cewa mace me neman daukar ciki ta ci dan samun ciki cikin sauri.