Sha’awa halittace a jikin kowane dan Adam, kuma kamar yanda kuke ganin wani dogo wani gajere, haka itama sha’awa karfi-karfi ce, ta wani tafi ta wani.
Kuma maganar gaskiya babu wani maganin yawan sha’awa na likita da za’a baka a ace kasha.
Saidai mazon Allah (SAW) ya baiwa matasa da basu da halin yin aure shawarar su riki yin azumi saboda yana dakushe sha’awa.
Amma muddin mutum lafiyarsa qalau kuma zai ci ya koshi kuma yana cikin kwanciyar hankali dolene ya ji sha’awa.
Ita sha’awa wata jarabawa itama daga Allah ga dan Adam domin a ga kokarinsa wajan amfani da ita ta hanyar da ya dace, kamar dai yanda dukiya da talauci suke jarabawa ga dan Adam.
Kaine da kanka zakawa sha’awarka linzami kada ta kaika ga halaka ko kuma ka biyata ta banyar da bata dace ba.
Hanyoyin da za’a bi dan rage karfin Sha’awa sun hada da :
Aure.
Azumi.
Gujewa Abokan Banza.
Daina kallace-Kallacen Fina-finan Batsa.
Abuta da zama da mutanen kirki.
Allah ya bada iko.