Idan ciki ya kai sati 20, gwajin Ultrasound yakan iya nuna cikin macene ake dauke dashi ko Namiji.
Hakanan akwai gwajin Amniocentesis da shima ake yi wanda ke nuna jinsin jaririn da ake dauke dashi.
Bayannan akwai alamu na gargajiya da ake amfani dasu wajan ganewa ko hasashen cikin mace.
Ciki Yayi sama: Wasu na cewa idan ciki yayi sama sosai, to wannan alamace dake nuna cewa diya macece za’a haifa.
Girman Nono: Hakanan akwai bayanan dake cewa idan nonon mace na hagu yafi na dama girma shima alamace dake nuna mace za’a haifa ba Namiji ba.
Ciwon Safe: Ciwon safe na daya daga cikin dalilan da ake alakanta cikin diya mace dashi inda me ciki zata rika jin kamar zata yi amai, kasala da sauransu.
Kalar Fitsari: Hakanan akwai bayanan dake nuna cewa kalar fitsarin mace ya zama kalar dorawa ba me duhu ba shima yana nuna alamar diya mace za’a haifa.
Saurin Fushi: A kwai kuma wani hasashe dake cewa mace me ciki dake da saurin fushi,alamace dake nuna cewa diya mace zata haifa.
Saurin Bugawar Zuciyar abinda ke ciki: Akwai kuma masu cewa idan abinda ke cikin mace yana nuna alamar saurin bugawar zuciya to wannan alamace ta cewa me ciki na dauke da cikin macene.
Yawan Maski a Fuska: Idan ya zamana mace me ciki na ganin yawan maski a fuskarta to wannan ma ana alakantashi da cewa tana dauke da cikin macene.