Shinkafa Cupi biyu
cup Wake rabin
Dan gishiri
Albasa
Man gyada
Tumatir
Yaji dakan hannu
Maggi
Salak
Cucumber
Dan lemun tsami
Da farko na dafa waken almost ya kusan nuna. Idan ba pressure pot idan zan dafa wake Ina yayyanka albasa akai kam na dafa yana da shi ya nuna da sauri
Na wanke shinkafata na zuba akai tare da gishiri. Sai ki rufe. Har sai ya dahu
Zaki yayyanka Albasarki iya yadda kikeso sai ki soya da mai
Sai ki yayyanka lettuce dinki dasu cucumber da tumatir. Daman already kin Riga da kin wanke su
Shikenan sai a sauke shinkafar a zuba a plate tareda sosayyiyar albasa da mai sai a zuba salak din aci dadi lfy a kira da lemu mai sanyi ko ruwan sanyi