Wednesday, January 8
Shadow

Aƙalla mutum 95 sun ràsù a girgizar ƙasa a China

Wata mummunar girgizar ƙasa ta afku a kusa da iyakar Tibet da Nepal.

Aƙalla mutum 95 ne aka tabbatar da mutuwarsu, sannan sama da 130 sun jikkata a girgizar, wadda ta afku a ranar Talata.

Girgizar ta kuma ƙetara zuwa yankin Nepal da ke ƙasar Indiya, wanda ke maƙwabtaka da Tibet na ƙasar China.

Girgizar ƙasar ta lalata gine-gine a birnin Shigatse na Tibet, lamarin da ya sa jama’a su riƙa kwararowa kan tituna domin tsira.

Tuni sojojin ƙasar suka fara aikin ceto, inda suka aika jirage marasa matuƙa zuwa wani yanki mai nisa a kusa da tsaunin Everest.

Karanta Wannan  Dan Wasa Mbappe Ya Ji Rauni A Karan Hanci A Wasan Da Suka Yi Da Austria

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *