Manyan ‘yan kasuwar man fetur su A.A Rano, AYM Shafa da Matrix Petroleum Services Limited sun kai Aliko Dangote kotu inda suke bukatar kotu kada ta amince masa da bukatar da yayi na a hanasu siyo man fetur daga kasashen waje saidai su siya a hannunshi.
Dangote dai ya shigar da ‘yan kasuwar da NNPCL kotu inda yake neman kotun ta hana shigo da man fetur daga kasar waje a rika saya daga hannunsa.
Dangote yace kawai ya kamata a shigo da man fetur Najeriya ne idan babu shi a matatarsa ko idan an samu karancinsa.
Saidai su kuma ‘yan kasuwar sun bayyana cewa Dagote na son ya zama shi kadai ne ke rike da harkar man a kasarnan wanda haka ba zai haifarwa kasuwar da mai ido ba.
Sun ce idan aka baiwa Dangote wuka da nama na harkar zai zama shi kadai ne ke kayyade farashin wanda hakan bai kamata ba ya kamata ace ana barin kasuwa ta halinta.
Hakanan suka ce idan Dangotene kadai ke samar da man fetur a kasarnan duk sanda aka ce matatar tasa ta tsaya da aiki ko an samu karancin man mutane zasu sha wahala.
Hakanan sun kara da cewa, a halin da ake yanzu ma Dangoten bai iya samar da isashshen man fetur din da zai wadaci kasarnan.
Kotun dai ta saka ranar January 20, 2025 dan ci gaba da sauraren Shari’ar.