
Shugaban kungiyar matasa ta AYCF ya jaddada cewa bai dace a riƙa yanke hukunci kan nasarorin Tinubu ba, duba da cewa bai kammala shekara biyu a ofis ba. Ya roƙi masu sukar gwamnatin Tinubu da su bari ya kammala wa’adin farko kafin su yanke mata hukunci.
“Tun farko mun san wa’adin Tinubu zai kasance mai wahala. Ya gaji ƙalubale da ba za a iya warware su cikin shekara guda ba. Ka da mu tayar da jijiyoyin wuya kawai saboda wasu mutane ba su samu muƙaman da suke so ba.”