Saturday, March 22
Shadow

A cikin Azumin Watan Ramadana, An kama dan shekaru 35, Abdullaziz Mohammed da yiwa karamar yarinya me shekaru 5 fyade a jihar Adamawa

‘Yansanda a jihar Adamawa sun kama dan shekaru 35 Abdullaziz Mohammed da zargin yiwa karamar yarinya me shekaru 5 fyade a jihar.

Kakakin ‘yansandan jihar, CSP Suleiman Nguroje ne ya bayyana haka inda yace lamarin ya farune a karamar hukumar Mubi dake jihar.

Yace mahaifin yarinyar me ya kai musu kara ranar March 17, 2025 inda yace Abdulaziz ya ja diyarsa zuwa cikin wani dakin da ake Nika a Kasuwar Barkono dake Mubi ya mata fyade.

Tuni dai aka tafi da yarinyar zuwa Asibiti.

Yayin da shi kuma wanda ake zargi ya amsa laifinsa.

Kwamishinan ‘yansandan jihar yayi Allah wadai da lamarin inda ya aika da wanda ake zargi zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar.

Karanta Wannan  DARASIN RAYUWA: Fitacçìyaŕ 'Ýar Tiktok, Khadija Gulma Ta Makançè

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *