Friday, January 16
Shadow

A hukumance: Aishatu Binani ta koma jam’iyyar haɗaka ta ADC

‘Yartakarar gwamnan jihar Adamawa a zaɓen 2023, Sanata Aishatu Ɗahiru Binani, ta yanki katin jam’iyyar haɗaka ta African Democratic Congress (ADC).

An ga tsohowar ‘yarmajalisar dattawan da ta wakilci mazaɓar Adamawa ta Tsakiya cikin wani bidiyo tana jawabin nuna goyon baya ga ADC, yayin da take zagaye da matasa.

“Mu mun ɗauki jam’iyyar ADC kuma za mu yi tafiya a cikinta,” in ji ta. “Muna roƙon Allah ya taimake mu ya raba mu da mutanen da muke tafiya da su amma suna gurɓata jam’iyya.”

Bayan kammala jawabin ne kuma aka gan ta ɗauke da katin jam’iyyar cikin wasu hotuna.

Binani ta yi takara ne a jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, inda ta gwada wa Gwamna Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP zazzafan ƙalubale a zaɓen na 2023.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Peter Obi ba zai taba zama shugaban kasa ba sai idan ya yadda ya fara zama mataimakin shugaban kasa>>inji Fasto Ayodele

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *