
A karin farko a tarihi, Musulmi me suna Zohran Mamdani ya lashe zaben fidda gwani na tsayawa takarar magajin garin birnin New York City dake kasar Amurka.
Zohran ya lashe zabenne a karkashin jam’iyyar Democrats inda ya doke tsohon gwamnan Jihar ta New York, Andrew Cuomo.
Zohran dan shekaru 33 ne kuma dan majalisa ne a Queens dake New York din.
A yanzu dai zai jira zuwa watan Nuwamba inda za’a gudanar da ainahin zaben dan ganin wanene zai zama magajin garin na Birnin New York City.
Saidai tuni yahudawan dake birnin suka ce zasu fice daga birnin sanoda nuna kiyayya ga Zohran.
Kuma wasu rahotanni sun bayyana cewa, Zohran yace idan ya zama magajin garin New York City, toh lallai duk sanda Firaiministan Israyla, Benjamin Netanyahu ya shiga birnin zai kamashi.