
Tsohon gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana rashin amincewarsa da dakatar da gwamnan jihar Rivers da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi.
Saidai bayyana ra’ayin nasa na zuwane bayan da ake ta tambayar ina ya shigene yayin da ake jin ta bakin manyan ‘yan Adawa akan lamarin?
Kwankwaso yace ya dakata ne ya ga wanda ke da ruwa da tsaki a cikin lamarin sun yi abinda ya dace shiyasa yayi shiru bai ce komi ba da farko.
Saidai yace a yanzu yana Allah wadai da wannan mataki inda yace majalisar tarayya ta zama ‘yan amshin shata da ba’a taba samun kamarsu ba a tarihin mulkin Najeriya.
Yace sune ya kamata su rika dawo da shugaban kasa kan hanya idan ya aikata ba daidai ba amma gashi sun zama ‘yan amshin shata.
Kwankwaso yace shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya mayar da Najeriya baya inda ya cire zababbun shuwagabanni ya dora sojoji abinda an wuce hakan a shekarun baya.
Kwankwaso yace Rikicin jihar Rivers bai kai matsayin da za’a ce har an dakatar da gwamna ba.