
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa, Gwamnatinsu ta APC bata tabuka abin a zo a gani ba a kudancin jihar kaduna.
Ya bayyana hakane a matsayin suka ga gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai.
El-Rufai ya shafe shekaru 8 yana a matsayin gwamnan Kaduna saidai a kwanannan ya bar jam’iyyar APC zuwa PDP.
A ci gaba da bayaninsa, Kashim Shettima ya bayyana cewa, Amma gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta canja akalar yankin inda ta kawo mai ci gaba.
Ya bayar da misali na ci gaban da gwamnatin Tinubu ta kai yankin kudancin jihar Kaduna inda yace kwanannan Shugaba Tinubun ya sakawa kudirin dokar samar da jami’ar kimiyya da fasaha ta Federal University of Applied Sciences hannu wadda za’a bude a karamar hukumar Kachia.