
Tsohon Hadimin Shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad ya bayyana cewa a Tarihi, Wanda basu da addini masu bautar Gumaka ne ke binne gawarwakinsu a cikin akwatin gawa na Zinare.
Yace a dokokin Addinin Kiristoci babu inda aka ce a binne gawa a cikin akwatin Zinare.
Ya bayyana hakane a matsayin Martani ga wani fasto a jihar Bayelsa da ya binne Mahaifiyarsa a cikin akwatin gawa na Naira Miliyan 150 wanda aka ce da gwal aka yishi.