
Hukumar kula da masu bautar kasa a Najeriya, NYSC ta baiwa matasa masu bautar kasar tabbacin cewa, a watan Maris zasu fara ganin karin Alawus zuwa Naira 77,000.
Shugaban hukumar, Brigadier General Olakunle Oluseye Nafiu ne ya bayyana hakan a yayin ganawa da matasan masu bautar kasa a ranar Alhamis.
An yi taron ganawar ne a Wuse da Garki a Abuja.
Brigadier General Nafiu ya bayar da tabbacin cewa Gwamnatin tarayya da Hukumar ta NYSC na kokarin ganin sun jiyawa matasan masu bautar kasa dadi.