Friday, December 5
Shadow

ABIN MAMAKI: Ji yanda ake zargin ‘Yan Ķasar Indiýa Sùn Ķori ‘Ýan Nijeriya Daga Nìjeriya

ABIN MAMAKI: ‘Yan Ķasar Indiýa Sùn Ķori ‘Ýan Nijeriya Daga Nìjeriya.

Ɗan jarida Nasiru Zango ya rubuta yana mai cewa wannan hoto da kuke gani dake nuna wasu matasa biyu da ‘yan sandan Nijeriya ke neman su ruwa a jallo ba kayan kowa suka sata ba kuma ba su yiwa kowa komai ba, babban laifin su bai wuce kasancewar su jajirtattun matasa masu neman abin kan su ba ta hanyar da dokar Nijeriya ta tanada, sai kuma watakila dan sun kasance masu karamin karfi da suka ki yadda wani babban kamfani ya zo har kasar su yana kokarin murkushe su ba.

Fiye da shekara kenan wani babban kamfani na ‘yan asalin Indiya ya yi karar wadannan matasa wadanda sune suke da mallakin kamfanin ganyen shayin Y and Z kan cewar sun satar musu samfurin ganyen shayin su (kamar yadda Coca Cola suka taba yin karar Pop Cola).

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Da Trump najin Hausa da ya sha Raddi a wajena amma tunda baya ji shikenan>>Inji Rarara

Amma da aka bincika a ofishin trade mark sai aka tabbatar da cewar Y and Z sun bi duk wata ka’ida hasali ma hukumar ce ta ba su rijista da wannan suna da tambarin da suke amfani da shi.

Amma abin takaici wadannan indiyawa wadanda ke ganin suna da karfi suna ta biye-biye kan lallai sai sun ci zarafin Wadannan matasa idan har basu Yi saranda sun daina wannan Sana’a ba.

Tun wancan lokaci ake ta kai kawo har sun fara gajiyar da matasan, amma abin mamaki wai kare da tallan tsire jami’ai na ta basu kariya da kokarin muzgunawa Wadannan matasa ta hanyar Yi musu barazana irin wannan.
Kun san dai yadda me Karfi ke fin kwarjin a idon galiban Mahukuntan kasar Nan

Karanta Wannan  Bidiyo: Ko ka yafewa Buhari ko ka zageshi sai Allah ya mai Hisabi akan abinda yayi daidai da inda bai yi daidai ba>>Inji Malam

Ina rokon Babban sufeton yansandan kasar nan IGP Kayode Egbetokun da ya shiga maganar nan da Kansa domin tabbatar da adalci da kaucewa yin amfani da karfin iko wajen muzgunawa Masu karamin karfi.

Nayi mamakin ganin yadda Jami’an yansanda suka Yi uwa da makarbiyya cikin wannan lamari tare da yada hotunan Wadannan matasa kai kace abokan Turji ne, kullum Kira ake ga matasa su kama Sana’a amma kuma babu wani cikakken tsari na kare mutumcin ka,Ban sani ko dan matasan yan arewa ne tun da dai wani lokacin an fi mai da su karkatacciyar kuka.

Ina kira ga mai girma DSP Barau I Jibril da sauran yan majalisu da ma duk wani me hali da yayi amfani da matsayin sa wajen taimakon Wadannan matasa yan Kano.

Karanta Wannan  Matashi Bilal Villa Ya Samu Kwangilar Naira Milyan Goma, Inda Ya Zama Ambasada Ta Wata Makarantar Koyon Crypto

Idan baku mance ba kamar yadda na faro a farko kamfani Pop Cola ma ba Dan Masu shi gwaskaye ba ne da yanzu Suma Ana Fama da su, domin yanzu ko kana da gaskiya Akan iya amfani da iko wajen muzguna maka har kaji cewar Ma ka hakura da kasuwnacin ka kawai saboda wani yana ganin cewar baka isa kayi irin nasa ba.

Dan Allah yan uwa ku taimaka da Neman hakkin wadannan matasa ta hanyar Kira ga IGP da Majalisun kasar nan da su shiga maganar domin ñeman halak ba laifi bane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *