
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi ya bayyana cewa, abin Takaici ne irinnyanda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya ware Naira Biliyan 712 dan gyaran filin jirgin sama a yayin da Miliyoyin ‘yan Najeriya ke fama da yunwa.
Yayi wannan maganane a yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke gargadin cewa mutane Miliyan 34 a Najeriya na cikin hadarin fadawa matsalar yunwa.
Peter Obi yace mutanen da Yunwa kewa barazana ‘yan uwan mu ne, makwabtan mu ne kuma abokan mu ne, yace abin takaici shine a irin wannan hali ne gwamnati zata ware biliyoyin Naira ba dan ciyar da talaka ba sai dan gyaran filin jirgin sama.
Obi yace a shekarar 2013 An ranto dala Miliyan 500 inda aka gyara manyan filayen jiragen saman Najeriya, dake Lagos, Abuja, Kano, Port Harcourt, da Enugu.
Yace dan haka ba lallai ana bukatar sake gyara filayen jirgin saman ba.
Obi yace kamata yayi a baiwa kula da rayuwar al’umma muhimmanci fiye da komai.