
Malamin Addinin Islama, Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun ya bayyana rashin jin dadinsa game da wa’azin Izala da aka yi a jihar Kebbi amma ba’a yi maganar matsalar tsaron yankin ba.
Malam yace mutane sun fi 100 da suka kirashi suna nuna damuwa akan Lamarin.
Malam yace kuma an yi hakane wai dan kada a batawa Gwamnati rai.
Yace suma suna tare da wasu jami’an Gwamnatin amma hakan ba zai hanasu fadar gaskiya ba.