Monday, December 15
Shadow

Abin Takaici ne Yàqìn Tshàgyèràn Dhàjì na jihar Borno yafi Yàqìn Basasa na Najeriya dadewa>>Inji Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana rashin jin dadinsa kan yanda yace yakin Bòkò Hàràm ya fi Yakin Basasar Najeriya dadewa.

Yace yakin basasa ya dauki watanni 30 ana yinsa duk da sun yi tsammanin ba zai wuce watanni 6 ana yi ba, yace amma gashi yakin Bòkò Hàràm yanzu ya kai Najeriya Shekaru 15 ana yinsa.

Yace ya je jihar Borno dan binciken dalilin Kafuwar Kungiyar inda yace ya samu cewa an so a yi sulhu dasu suka kiya amma daga baya suka yadda saidai sulhun ya ruguje bayan da gwamnati ta kasa ganawa da shuwagabanninsu.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Rawar da Ali Nuhu ya tika da Rahama Sadau ta sa ana ta cece-kuce inda wasu ke cewa, wai yaushe zai girma?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *