Thursday, May 22
Shadow

ACF ta buƙaci ƴan Najeriya su shirya fuskantar ambaliya a bana

Ƙungiyar tuntuɓa ta arewacin Najeriya wato ACF ta yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da ƴan ƙasar da su fara shirin fuskantar ambaliyar daminar bana.

Ƙungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar a matsayin martani kan hasashen ambaliya ta shekarar 2025 da hukumar kula da yanayi ta fitar, inda a ciki hukumar ta lissafa garuruwa aƙalla 1,249 a ƙananan hukumomi 176 da ke jihohi 30, ciki har da jihohi 16 na arewa za su fuskanta.

A wata sanarwa da sakataren watsa labarai na hukumar, Farfesa Tukur Muhammad-Baba ya fitar, ƙungiyar ta nuna damuwarta kan yiwuwar faɗaɗar ambaliyar, da fargabar yadda za ta jawo tsaiko a harkokin rayuwa da walwalar al’umma yankin.

Karanta Wannan  Ina goyon bayan kudirin dokar canja fasalin karba da raba Haraji a Najeriya>>Inji Bishop Kukah

Ƙungiyar ta ce ta ga ƙoƙarin gwamnatin tarayya na wayar da kan al’umma kan batun ambaliyar, amma ta ce ƙoƙarin bai fito fili sosai ba, musamman a yanzu da damina ta fara kankama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *