Malam Surajo Yarima ya ce a lokacin da aka kai karar kotu ya samu karaya ne inda yake jinya a jihar Adamawa, kuma ya nuna musu hotunan lokacin da yake jinya domin su zama hujja, amma duk da haka ba a karbi uzurinsa ba.
Ya ce yanzu haka an watsar da kayan su waje, inda ba su wajen kwana duk da cewa yana mata da hara tara.
Don haka ne Yarima ya roki gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya kai masa ɗauki domin shiga lamarin.