Saturday, May 24
Shadow

Akpabio ya kai Sanata Natasha Akpoti kara kotu kan takardar Hakuri da shagube data yi masa, Yace yana son Kotu ta sa Natasha ta goge Wasikar a shafinta na sada zumunta sannan ta bashi Hakuri

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya maka Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a kotu, yana zargin ta da wallafa kalaman ɓatanci a cikin wata wasikar bada haƙuri da aka danganta da ita — Wasikar da ke ɗauke da wata magana mai cin mutunci da ke cewa “ta yi kuskuren tunanin cewa kujerarta a Majalisa ta samu ta hanyar zaɓe, ba ta hanyar jima’i ba.”

Rahotanni sun bayyana cewa wannan ƙara ta samo asali ne daga wata wallafa da ke yawo a kafafen sada zumunta, wadda aka danganta da Sanata Natasha, inda ta nemi gafara daga Shugaban Majalisar bisa wasu maganganu da ake cewa ta furta a baya. A cikin wannan wasikar, an ambaci cewa ta “yi kuskuren ɗauka cewa ta samu kujera ne ta hanyar sahihin zaɓe.”

Karanta Wannan  Ku yiwa Najeriya addu'a, Matar shugaban kasa, Remi Tinubu ta gayawa musulmai da suka fara Azumin watan Ramadana

Lauyoyin Akpabio sun ce wannan magana ta wallafa ra’ayi mai matuƙar cin mutunci da bata suna ga shugaban majalisar, kuma hakan ya saba wa dokar ƙasa game da ɓatanci da cin mutunci ta hanyar kafafen yaɗa labarai.

KBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *