Monday, May 5
Shadow

Akwai ƴanƙasar waje da ke kai hari a Benue – Alia

Gwamnan jihar Benue da ke tsakiyar Najeriya, Hyacinth Alia ya yi zargi cewa maharan da suka kai hari jihar ba ƴan Najeriya ba ne.

Gwamnan ya faɗi hakan ne a wani shirin gidan talbijin na Channels, inda ya ce maharan na magana ne da wata irin Hausa da Fulatanci wanda ba irinsu ake yi a ƙasar ba.

“Waɗannan mutanen sun zo ne a shirye da makamansu da bindigogi ƙirar AK-47 da 49. Kuma ba su yi kama da ƴan Najeriya ba, ba sa magana kamar yadda muke yi, Hausarsu ba irin ta mu ba ce. “

Inda ya ƙara da cewa daga bayanan sirrin da suka samu daga mazauna yankunan da aka kai hare-hare, ya nuna cewa maharan ƴanƙsar waje ne.

Karanta Wannan  Da Duminsa:APC ta gayawa Gwamna Fubara na jihar Rivers ko dai ya ajiye mukaminsa salin Alin ko a tsigeshi

Hakan na zuwa ne bayan wata ziyarar nuna alhini da mai baiwa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya kai jihar.

Inda ya bai wa al’umomin jihar tabbataci kan matakan da ya ce gwamnatin na ɗauka domin magance matsalar tsaro a ƙasar.

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da ake zargin wasu ƙungiyoyin ƴanbindiga na ƙasashen waje na kai hari wasu sassan ƙasar.

Kamar ƙungiyar Lakurawa da ke kai hare-hare a jihohin Sokoto da Zamfara da ke arewa-maso-yammacin ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *