
Mawallafin jaridar Ovation Magazine, Dele Momodu ya bayyana cewa, akwai alkawari tsakanin Atiku Abubakar da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo kan cewa, Obasanjo zai yi mulkin wa’adi daya ne ya sauka ya baiwa Atikun.
Saidai Obasanjo be cika wannan alkawari ba.
Dele Momodu yace duk da wannan Atiku bai daina baiwa Obasanjo girmansa ba duk da cewa yana da goyon bayan gwamnoni a wancan lokacin.
Dele Momodu yace daga karshema Obasanjo sawa yayi aka kwace abubuwan da kundin tsarin mulki suka tanada a baiwa Atiku.
Yace amma Atiku sai ya mayar da hankali akan kasuwanci, kuma yayi ta samun ci gaba, yace da sauran ‘yan siyasa sun kasance irin Atiku masu sana’a da Najeriya bata samu kanta a halin da take ciki yanzu ba.