
Haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu fataucin dabbobi da kayan abinci a Najeriya, ta ce akwai fargabar dabbobi za su iya yin tsada a lokacin babbar sallah.
Sun ce hakan zai iya faruwa ne saboda takunkumin da gwamnatin Nijar ta saka na haramta fitar da dabbobi zuwa ƙasashen waje.
Ƴan kasuwar sun roki hukumomin Nijar su kalli maslahar al’umma su cire haramcin.
Shugaban ƙungiyar, Dakta Muhammad Tahir ya shaida wa BBC cewa za a samu koma-baya a harkar sayar da dabbobi.
“Idan gwamnatin Nijar tana ganin matakin da ta ɗauka shi ne zai kawo saukin abubuwa, to gaskiya akwai matsala, saboda ƴan Nijar da ke hada-hadar dabbobin idan ba su samu mai saye ba babban koma-baya ne,” in ji shi.
Ya ce akwai shanu da raguna sama da 50,000 waɗanda aka saya daga Chadi, inda yanzu haka suke maƙale a iyakar Chadi da Nijar.
“Gaskiya za a samu matsala. Muddin aka ɗauki tsawon lokaci ba a shigo da dabbobi daga Chadi ko Nijar ba to za a iya samun tashin gwauron zabi na dabbobi a kasuwannin mu. Mu kuma ba mu fatan haka,” in ji Dakta Tahir.
Nijar dai na sahun gaba wajen fitar da dabbobi zuwa wasu ƙasashe musamman maƙwabta.
Hukumomin ƙasar sun ce sun ɗauki matakin haramta fitar da dabbobin ne don samar da rahusa a lokacin babban sallah.