Monday, May 5
Shadow

Akwai rashin hankali a kashe-kashen jihar Filato – Gwamnonin arewa

Ƙungiyar gwamnonin arewacin Najeriya ta yi Allah wadai da kashe-kashen da wasu mahara suka yi a garuruwan Ruwi da Manguna da Daffo da Josho da Hunti da ke ƙaramar hukumar Bokkos ta jihar Filato, inda ta bayyana kisan da na rashin hankali.

Shugaban ƙungiyar, gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ne ya bayyana haka, inda ya ce harin – wanda ya ci rayukan mutane da dama tare da jikkata wasu ciki har da mata da ƙananan yara – yana bazarana ga zaman lafiya da ci gaban yankin arewacin ƙasar.

A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Ismaila Uba Misilli ya fitar, gwamnan ya ce, “rayuwar ɗan’adam na da daraja da ta wuce a wulaƙanci,” in ji shi kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Karanta Wannan  Hoto: An kama janar din soja inda aka kulleshi a Abuja saboda karkatar da shinkafar tallafi da sayar da motocin aiki da janare na ofishinsa

Gwamna Inuwa ya kuma yaba da ƙoƙarin gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang bisa matakan da ya ɗauka, sannan ya yi kira ga jami’an tsaro su ƙara ƙaima wajen kamo waɗanda suke da hannu a kashe-kashen.

“A matsayinmu na gwamnonin arewa, za mu cigaba da ƙoƙari domin kawo ƙarshen rikice-rikicen da suka dabaibaye yankin.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *