
Rahotanni sun bayyana cewa, akwai yiyuwar Najeriya ta fada matsalar karancin man fetur saboda masu dakon man fetur din sun dakata da dakonsa.
Direbobi masu dakon man fetur din sun dakata da dakon man ne saboda zargin cin zarafinsu da ake yi da sukawa hukumar gwamnatin jihar Legas da ma’aikatar sufuri ta tarayya.
Hakanan suma masu kamfanonin sadarwa sun yi gargadin cewa, za’a iya samun matsalar sabis idan direbobin dakon man suka daina daukar man saboda dashi suke amfani wajan gudanar da ayyukansu.
Jaridar Punchng ta bayyana cewa a ranar Asabar da Lahadi da suka gabata direbobin man sun ki daukar man fetur din.
Shugaban kungiyar direbobi ta NARTO Yusuf Othman ya bayyana cewa wannan lamari yayi kamari dan kuwa mahukuntan jihar Legas na kama musu motoci suna tafiya dasu ofis, suna duka direbobinsu suna kuma lalata motocin.
Yace ya kamata a hada hannutare su da gwamnatin jihar Legas din a yi aiki tare dan kuwa idan babu direbobin su kansu ba zasu iya yin aiki ba.
A bangaren jihar Legas kuwa, babban sakatare a ma’aikatar sufuri ta jihar, Wale Musa ya bayyana cewa suna tabbatar da doka da oda ne kuma babu wanda zai hanasu yin aikinsu.
Yace ba zasu bari a rika kawo tsaikon ababen hawa a inda bai kamata ba.