Friday, December 5
Shadow

Akwai yiyuwar fadawa wahalar man fetur a Najeriya saboda motocin dakon man sun dakatar da daukar man Fetur a matatar Dangote

Rahotanni daga Legas na cewa kungiyar Direbobi ta (NARTO) ta bayar da Umarnin dakatar da dakon man fetur a matatar Dangote.

Hakan na zuwane yayin da aka fito da wani sabon salon karbar Haraji daga Direbobin a Legas.

Hakan na nufin idan ba’a warware wannan matsala ba nan da awanni 24 zuwa 48, to akwai yiyuwar za’a fada matsalar karancin man fetur a fadin Najeriya.

Shugaban kungiyar, Mr. Yusuf Lawal Othman ya bayyana cewa ba zasu biya sabon harajin na Naira 12,500 ba.

Yace kungiyarsu Naira N2,500 zasu iya biya akan kowace mota ba zasu iya biyan Naira dubu 12,500 ba.

Yace kuma dukkan yunkurin tattaunawa yaci tura.

Karanta Wannan  Amurka ta fara janye sojojinta daga jamhuriyar Nijar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *