
Rahotanni sun bayyana cewa, akwai yiyuwar gwamnatin tarayya ya sake sayar da kamfanin rarraba wutar Lantarki na Discos.
Hakan na kunshene a cikin wata sabuwar doka dake gaban majalisa da sukw kokarin zartaswa.
Tuni ‘yan majalisar suka fara shirin zartar da kudirin dokar wadda zata bukaci ‘yan kasuwar dake rike da kamfanonin Discos din su inganta wutar ko kuma a sayarwa da wasu.
Sanata Enyinnaya Abaribe ne ya gabatar da kudirin dokar a zauren majalisar.