Za’a iya game cewa Azzakari ya mutu idan ya zamana cewa baya iya mikewa da kyau ta yanda mutum zai iya yin jima’i ya gamsu.
Hakanan idan ya zamana mutum baya jin sha’awa, ko kuma karfin sha’awarsa ta ragu sosai, shima za’a iya cewa Azzakarinsa ya mutu.
Amma idan ya zamana cewa yau mazakutarka ta mike gobe ta ki mikewa, wannan ba matsalar mutuwar azzakari bane, idan ya zamana bata mikewa da kyau ne ta yanda zaka gamsu ko kuma baka dadewa Sam kake kawowa to ya kamata a nemi likita.
Abubuwan dake kawo mutuwar Azzakari sun hadada:
Yawan kiba.
Ciwon Sugar ko Diabetes.
Ciwon zuciya.
Yawan kitse a jiki.
Rashin kwanciyar hankali.
Damuwa.
Rashin Samun isashshen bacci.
Shan giya.
Shan taba da sauransu.
Ana magance matsalar mutuwar Azzakarine ta hanyoyin:
- Motsa jiki
- Daina Shan taba.
- Rage yawan damuwa.
- Daina shan giya.
- Samun wadaccen bacci.
- A nemi shawarar likita.