Saturday, March 15
Shadow

Alawus din da kuke dauka me yawa da yanda kukafi kowa kudi na baiwa ‘yan Najeriya haushi sosai>>Batist Church ta gayawa Tinubu

Kungiyar Baptist church dake Abuja sun caccaki gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu inda suka bukace shi yayi wani abu game da yunwa da matsin rayuwa dake damun ‘yan Najeriya.

Cocin ta bayyana hakane a yayin taron cikarta shekaru 10 da kafuwa a Abuja inda manyan baki a wajan suka soki irin rayuwar kece raini da ‘yan siyasa ke yi yayin da su kuma talakawa aka barsu cikin halin kaka nikayi.

Daya daga cikin wadanda suka yi magana a wajan taron zhine Reverend Dr. Israel Akanji inda yayi kira ga gwamnati data kawo tallafi a bangaren Ilimi, da lafiya da noma.

Yace ‘yan Najeriya da yawa na daf da fadawa matsalar yunwa da zata iya kaisu ga halaka. Yace suna yabawa da kokarin da gwamnati take yi amma akwai bukatar a kara kaimi.

Karanta Wannan  Mun baiwa Shugaba Tinubu shawarar ya ƙara kudin haraji na VAT daga kashi 7.5% zuwa kashi 10% -inji Oyedele, shugaban Kwamitin Haraji na Najeriya

Yace Alawus masu yawa da ‘yan siyasa ke dauka da kuma yanda tazara tsakaninsu da talakawa ke kara fadada abin yana damun ‘yan Najeriya da yawa sosai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *