Monday, December 16
Shadow

Albashin ‘yan majalisa baya wuce kwanaki 3 ya kare>>Inji Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara

Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ya bayyana cewa, Albashin ‘yan majalisar tarayya baya wuce kwanaki 3 ya kare.

Dogara yayi kira ga ‘yan majalisar da su bayyanawa ‘yan Najeriya kudaden da ake biyansu dan a daina musu kallon suna samun kudaden da ba haka bane.

Yace a lokacin da yake kakakin majalisa yana karbar kasa da Naira Dubu dari hudu a matsayin albashi.

Yace kuma yana karbar Miliyan 25 a matsayin alawus, yace bai taba yin amfani da alawus din ba, ya bude asusun ajiya na daban ne inda ya baiwa akawunsa umarnin ya rika yiwa mutane hidima da kudin kuma idan suka kare, ya rika rantowa.

Karanta Wannan  Akalla mutum 1,301 ne suka mutu a yayin aikin Hajjin bana – Saudi Arabia

Yace dama Albashi shine na dan majalisa a yayin da Alawus kuma na yiwa mutanen da suka zabeka aiki ne.

Ya bayyana hakane a wajan wabi taro a Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *