
Wani Sojan Najeriya me suna Muhammad ya koka da cewa, tun shekarar 2017 yake ta son ya ajiye aiki amma an hanashi.
Ya jawo hankalin shuwagabannin sojoji da ministan tsaro da Shugaban kasa da ‘yan majalisa a cikin Bidiyon nasa inda yace su taimaka masa ya ajiye aikin.
Yace a duk sanda yayi yunkurin ajiye aikin sai a rika masa hanyahanya.
Yace wata matsalar iyali ce ta sanyashi gaba shiyasa ya ke son ajiye aikin.