
Tauraruwar fina-finan Hausa, Fatima Hussain ta fito ta bayyana takaici kan garkuwa da dalibai mata 25 da aka yi a jihar Kebbi.
Ta bayyana hakane a shafinta na sada zumunta inda tace idan ba’a so a yi karatu ne a kulle makarantun mana.
Tace duka yaushe aka sace dalibai mata amma gashi an sake yi.
Tace daliban na da kananan shekaru.