
Kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Wilfred Ndidi ya ce a ci gaba da atisaye dan shirin wasan Najeriya da Algeria.
Inda yayi Alkawarin idan Gwamnatin Najeriya bata biya hakkokin ‘yan kwallon ba nan da ranar Asabar, shi zai biya.
‘Yan kwallon na super Eagles dai sun ce ba zasu yi Atisaye ba sai an biyasu hakkokin wasannin baya da suke bi.
Gwamnatin tarayya tuni tace an kammala komai na biyan ‘yan wasan hakkokinsu inda tace a yau Alhamis zuwa gobe ‘yan kwallon zasu fara jin Alert na hakkokin nasu.
Da yawa dai sun bayyana wannan lamari da abin Kunya.