A ranar Talata ne rahotonni suka fara ɓulla cewa mayaƙan ƙungiyar Islamic State of West Africa Province (Iswap) ta kashe Birgediya Janar Musa Uba a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Kisan nasa ya tayar da muhawara game da yadda ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi kamar Boko Haram da Iswap ke kashe manyan jami’an sojin Najeriya, duk da cewa ba shi ne na farko da ya mutu a filin daga ba.
Bayanai sun nuna cewa Janar Uba ne babban jami’i na biyu mafi girman muƙami da ‘yanbindigar suka kashe tun shekarar 2021.
Iswap ta bayar da sanarwar kisansa a shafinta na Telegram, inda ta ce mayaƙanta sun kama shi ranar 15 ga watan Nuwamba bayan harin kwanton-ɓauna da suka kai wa sojojin Najeriya a kusa da garin Wajiroko da ke jihar ta Borno.
Rundunar sojan Najeriya ta tabbatar da kai harin, inda ta ce an kashe sojojinta biyu da dakarun sa-kai biyu. Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya miƙa ta’aziyya ga iyalan Janar Uba da sauran dakaru.
Wannan maƙala ta duba manyan jami’an sojan Najeriya da aka kashe yayin yaƙi da Boko Haram tun daga 2018.
Birgediya Janar M Uba shi ne kwamandan birged na 25 na rundunar sojin Najeriya.
Uba, ya zamo jami’in sojin Najeriya mafi girman muƙami da ƙungiyar ta kashe tun daga shekarar 2021.
Borno na cikin jihohin Najeriya da suka fi fama da hare-haren masu iƙirarin jihadi, inda Boko Haram da sauran ƙungiyoyi ke iko da wasu yankuna.
A tsakiyar watan Janairu ma wasu mayaƙan Boko Haram ko na Iswap sun kai wa wasu manoma da masunta hari a garin Dumba na jihar ta Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Akasarin mazauna ƙananan hukumomin Gudumbari, da Marte, da Abadam na zaune ne ƙarƙashin ikon ‘yanbindigar kusan tsawon shekara shida.
Birgediya Janar Dzarma Zirkusu
Tun bayan fara yaƙin Boko Haram a 2009, Birgediya Janar Dzarma Zirkusu ne jami’in sojan Najeriya mafi girman muƙami da ya fara rasa ransa a 2021.
Janar ya mutu ne tare da wasu dakaru uku lokacin da shi ma mayaƙan Iswap, wadda ta ɓalle daga Boko Haram, suka yi musu kwanton ɓauna a garin Askira Uba a watan Nuwamban 2021.
Janar ɗin ɗan asalin jihar Adamawa ya zama kwamandan rundunar 28 Task Force Brigade a garin Chibok a watan Janairun shekarar.
Sanarwar da rundunar sojan Najeriya ta fitar a lokacin ta ce ta yi nasarar kashe ‘yanbindigar da dama da kuma ƙwace makamai masu yawa yayin da suka kare harin da aka kai musu.
Kanal Dahiru Chiroma Bako
