Friday, December 5
Shadow

ALLAH SARKI: Tsohuwar Ministar Jinkai, Sadiya Umar Farouq, Ta Fashe da Kuka Yayin Taron Addu’a na Musamman Ga Marigayi Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari

Ministar Jinkai a lokacin mulkin Buhari, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta kasa jurewa ta fashe da kuka yayin da take halartar taron addu’a na musamman da aka gudanar domin girmama marigayi tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, a Babban Birnin Tarayya Abuja.

Taron addu’ar, wanda ya ja hankalin fitattun ’yan siyasa, manyan malamai da jama’a daga sassa daban-daban na ƙasar nan, ya gudana ne cikin yanayi na alhini da jimami, inda aka roƙi Allah ya jikan marigayin da rahama tare da gafara, bisa irin gudunmawar da ya bayar wa ƙasa a lokacin da yake mulki.

Hajiya Sadiya, wadda ta kasance daga cikin amintattun masu rike da madafun iko a gwamnatin Buhari, ta kasa jure hawaye yayin da aka fara ambato irin jagoranci da tsayin daka da marigayin shugaban ya yi wajen kawo sauyi da tabbatar da ayyukan jinƙai a tsakanin talakawa.

Karanta Wannan  Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna zai koma aiki nan da kwana 10 – Minista

~KBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *