Monday, December 16
Shadow

Allah ya isa tsakanina da Hamster Kombat bazan taba yafe muku ba ko kabarinku na balbala da wuta>>Likitan da ya ajiye aiki a Zaria Saboda Hamster Kombat ya magantu

Ma’aikacin Asibiti a Zaria ta jihar Kaduna, Musa A Bello da ya ajiye aikinsa saboda tsammanin Hamster Kombat zasu bashi kudi da yawa yayi Allah ya isa.

Ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta inda yace wanda ya bashi shawarar yin Hamster Kombat yace masa da haka Bitcoin ya fara.

Yace abin takaici ne abinda hamsters Kombat suka bashi wanda bai taka kara ya karyaba inda ya ajiye aikinsa na shekara da shekaru saboda tsammanin zaau bashi kudi masu yawa.

Ya kara da cewa yanzu ta ina zai fara, daga barazanar da ake masa a wajan aiki ko da dariyar da jama’a ke masa?

Karanta Wannan  Gwamnan Kano Abba zai kori kwamashinonin da ba su da himma

Yace rayuwarsa a yanzu ta shiga halin rashin tabbas amma yace in Allah ya yarda zai sake samun wani aikin.

Yace ba zai taba yafewa Hamster Kombat ba saidai idan ya fito a farashin duk guda daya akan dala $100

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *