Thursday, December 25
Shadow

Allah ya riga ya kaddarowa Atiku ba zai zama Shugaban Najeriya ba dan haka ya hakura kawai>>Inji Sarkin Legas, Oba Rilwan Akiolu

Sarkin Legas, Oba Rilwan Akiolu ya bayyana cewa Allah ya riga ya kaddarowa Atiku Abubakar cewa ba zai zama shugaban kasar Najeriya ba.

Yayi kira ga Atiku da ya hakura da kaddarar da Allah ya doro masa cewa ba zai zama shugaban Najeriya.

Atiku dai tin a shekarar 1992 yake neman takarar shugabancin Najeriya amma bai samu ba.

Ya bayyana hakane ga manema labarai a fadarsa yayin da yake bikin cika shekaru 22 da hawa karagar sarautar Birnin na Legas.

Yace shi kuma Tinubu zabin Allah ne dan haka yana kira ga ‘yan Najeriya da su goya masa baya.

Karanta Wannan  Ni na yi imani, Waka halalce kuma wakar da nake yi zata kaini Alhannah, amma duk randa na gane waka Haramun zan daina yi>>Inji Ali Jita

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *