
Rahotanni daga kasar Amurka na cewa, an dauke wutar lantarki a kasar wanda ya jefa mutane 350,000 cikin Duhu.
Lamarin ya farune dalilin ruwa me tsanani da iska da aka yi a yankin Michigan.
Mahukunta sun yi gargadin cewa, mutane su kiyaye akwai yiyuwar ci gaba da ruwan da kankara.
Saidai wannan labarin yasa hukumar kula da wutar lantarki mamaki, inda har suka saka alamar ido a bude sosai a kafar X, watau Alamar abin ya basu mamaki kenan.
Da yawan ‘yan Najeriya sun ji haushin wannan lamarin inda suke cewa ai dauke wutar ba irin na Najeriya bane da ake yi kullun.