
Hukumomi a kasar Amurka sun daure malamar makaranta me suna Jacqueline Ma ‘yar kimanin shekaru 36 tsawon shekaru 30 a gidan yari saboda samunta da laifin yiwa dalibinta maza fyade.
A baya dai an bata kyautar karramawa a matsayin gwarzuwar malama a yankin San Diego County na kasar.
Saidai daga baya an kamata da laifin yiwa yara dalibanta fyade, kuma ranar Juma’ar data gabata ne aka yanke mata hukuncin shekaru 30 a gidan yarin.
Bayan yanke mata hukuncin, ta ashe da kuka inda tace tana fatan za’a yafe mata kuma tana danasanin bin son zuciya wajan batawa wadannan kananan yara Tarbiyya.