Wednesday, January 8
Shadow

An fara bincike kan harin da B0k0 Hàràm ta kai kan sojoji a Borno

Rundunar tsaron Najeriya ta ƙaddamar da bincike kan harin da ƴan Boko Haram suka kai wa sojojin ƙasar a sansaninsu da ke jihar Borno a arewa maso gabashin ƙasar.

Rahotanni sun ce harin na Boko Haram ya yi ajalin aƙalla sojojin Najeriya shida a sansanin sojojin da ke Damboa a ranar Lahadi, kamar yadda kafar AFP ta ruwaito, inda ta ce tsagin Boko Haram na ISAWP ne suka kai harin.

Kakakin rundunar tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba ya tabbatar da harin, amma bai bayyana adadin waɗanda aka kashe ba.

Sai dai ya ƙara da ecwa, “mun fara bincike kan lamarin. Za mu fitar da sanarwa game da harin nan kusa,” kamar yadda ya bayyana wa BBC.

Karanta Wannan  Gwamnin ban tausai:Ji yanda mutane suka nutse a ruwa yayin da suka shiga kwale-kwale dan tserewa harin 'yan Bin-di-ga a jihar Naina

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *