
Wasu kungiyoyin fafutuka sun yi Allah wadai da majalisar tarayya saboda cusa jimullar Naira Tiriliyan N10.96tn a cikin kasafin kudin Najeriya a tsakanin shekarun 2021 zuwa 2025.
Kungiyoyin sun bayyana hakan da cewa bai dace ba inda suka nemi hukumomin yaki da rashawa da cin hanci na Najeriya dasu yi bincike kan wannan zargin.
Kungiyoyin da suka yi wannan zargin sune the Socio-Economic Rights and Accountability Project, da kuma the Centre for Anti-Corruption and Open Leadership.
Kungiyar BudgIT ce ta fara yin wannan bincike inda tace jimullar ayyukan da aka cusa a cikin kasafin kudin sun kai 30,632.