An gano wani gidan Alfarma na miliyoyin daloli da tsohon me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro Sambo Dasuki ya saya a kasar Amurka.
Sambo Dasuki dai an kamashi bisa zargin cinye Biliyoyin kudade da aka ware dan yaki da kungiyar Boko Haram a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.
Sannan a wannan sabon bincike da ya bayyana an gano Dasuki yayi amfani da kudaden wajan sayen godajen Alfarma a biranen Los Angeles, California da kuma babbar unguwar masu kudi ta McLean, Virginia, dake babban birnin kasar Amurka, Washington, DC.
Wata kungiya dake bincike da kwarmaton yanda ake sace kudaden talakawa a kasar Afrika me suna (PPLAAF) ce ta gano lamarin.
Kungiyar tace wasu dake taimakawa Dasuki sayen gidajen alfarmar Robert da Mimie Oshodin sun karbi akalla Dala Miliyan 27 daga ofishij dasukin.
Saidai kungiyar tace kasar Amurka na nuna halin ko in kula game da batun cin hanci da rashawa yayin da a Najeriya kuma ba’a yin binciken da ya kamata kan irin wadannan zarge-zargen.
Gidan dai an ce ba wani zama Dasukin yake a cikinsa ba, kawai dai an siya an jiyene kamar kadara.