Thursday, May 29
Shadow

An gurfanar da wata mata Harira Muhammad a gaban babbar kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a Post Office a jihar Kano, bisa zargin ta da auren maza biyu a lokaci guda

Ita dai Hariri ta kwashe tsawon watanni 6 basa zaune waje ɗaya da mijinta na farko Sagiru Shuaibu Tudun Murtala, sai dai ya ce ranar da ya ziyarci gidanta, ya tarar da ita kwance a gadonsu na aure da wani, lamarin da ya sa ya sanar da makwabta abin da ke faruwa.

A lokacin da ta ke kare kanta game da zargin da mijinta na farko ya yi, Hariri ta musanta cewa akwai igiyar aure tsakaninta da shi, amma sai dai da alkalin kotun mai shari’a Khadi Munzali Tanko Soron-Dinki ya umarce ta data yi rantsuwa da Al-Qur’ani sai ta janye kalamanta.

Shi kuwa a nasa ɓangaren, Bello Abdullahi Ƴankaba mijin Harira na biyu, ya shaida wa kotun cewa ya aureta ne a hannun kawunta Abdullahi Umar kan sadaki naira dubu ɗari.

Karanta Wannan  Yarbawane suka fi kowace kabila a kasarnan yin gwajin DNA dan gano cewa ko matansu sun ci amanarsu ta hanyar basu 'ya'yan da ba nasu ba, Hausawa basu cika yin wannan gwaji ba

Bayan kammala jin dukkanin ɓangarorin, mai shari’a Khadi Munzali Tanko Soron-Dinki, ya bada umarnin a kai Harira da Bello Ƴankaba gidan yari har zuwa ranar 16 ga wannan watan, sannan  ƴansanda su ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *