Friday, March 28
Shadow

An kai karin jami’an tsaro dubu 10 Jihar Rivers bayan dakatar da Gwamna Fubara

Rahotanni daga jihar Rivers na cewa,karin jami’an tsaron Civil Defense dubu 10 ne aka kai jihar Rivers dan su samar da tsaro bayan dakatar da Gwamna Fubara.

Rahotannin sun ce an kai jami’an tsaronne dan su hadu da sojoji da sauran jami’an tsaron dake jihar dan su samar da tsaro ga bututun man fetur dake jihar.

Kakakin hukumar ta Civil Defense, Afolabi Babawale ya tannatar da hakan, yayi kira da a daina fasa bututun man inda yace jami’ansu dubu 10 ne aka kai jihar ta Rivers dan su hana hakan.

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dai ya dakatar da Gwamna Fubara bayan da aka fasa bututun man fetur a jihar har sau 3.

Karanta Wannan  Najeriya ta fada Duhu yayin da matsalar wutar lantarki ta sake aukuwa, Ji Jihohinnda lamarin ya shafa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *