
Rahotanni daga jihar Legas na cewa, ‘yansanda a jihar sun kama wani uba me suna Best Orji dan kimanin shekaru 39 da zargin yiwa ‘ya’yansa fyade.
Mahaifiyar yaran ce ta kai korafi wajan ‘yansandan inda tace ya aikata lamarin a yayin da yaran ke da shekaru 12 da 14.
Kakakin ‘yansandan jihar, (PPRO),CSP Benjamin Hundeyin ne ya tabbatar da hakan a sanarwar da ya bayar ga manema labarai.
Yace sun kama Best Orji zasu gurfanar dashi a gaban kuliya.