
Wasu ‘yan Arewa 89 da aka kama a Legas da zargin cewa mahara ne, hukumar ‘yansandan Najeriya ta fito tace ba mahara bane, ma’aikatan kamfanin Dangote ne.
Hukumar ‘yansandan Legas sun ce ma’aikatane aka kawo daga Katsina zasu yi aiki a matatar man fetur ta Dangote.
Kakakin ‘yansandan jihar Legas, CSP Benjamin Hundeyin ya tabbatar da cewa sun gudanar da bincike kuma sun gano ma’aikatan matatar man Dangote daga Katsina ba mahara ba.